Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhu na MDD ya tsawaita izinin daukar matakai kan safarar 'yan ci rani daga Libya
2020-10-03 16:52:50        cri
Kwamitin sulhu na MDD, ya sabunta izinin gudanar da bincike da kwacen jiragen ruwan da suka fito daga tekun Libya, domin magance safarar 'yan cin rani da sauran bil adama.

Kudurin kwamitin mai lamba 2546, da aka sabunta a jiya, wanda kuma daukacin mambobinsa 15 suka amince da shi, ya sabunta izinin da watanni 12 daga ranar da aka amince da shi.

Kudurin ya ba mambobin kwamitin damar binciken jiragen ruwan da suka fito daga Libya, wadanda suke da hujjar zargin ana amfani da jiragen wajen safarar bil adama. Har ila yau, ya bada damar kwace jiragen ruwa idan aka tabbatar ana amfani da su wajen gudanar da irin wadancan ayyuka.

Kudurin ya kuma yi tir da duk wani nau'i na safarar bil adama ta Libya, ko daga libyar da kuma gabar tekun kasar.

Kudurin ya bukaci Sakatare Janar na MDD ya ba kwamitin rahoton aiwatar da matakin, watanni kuma 11 bayan fara amfani da shi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China