Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakin tallafin matalauta na ba da inshorar jiyya ya samu nasara a kasar Sin
2020-10-15 10:30:05        cri

A jiya Laraba ne aka kira taron dandalin ba da inshorar jiyya don tallafawa matalauta, a jerin ayyukan ranar tallafin matalauta na shekarar 2020 na kasar Sin, inda rahotanni suka ce tun daga fara aiwatar da shirin tallafin matalauta na ba da inshorar jiyya na tsawo shekaru 3, wato daga shekarar 2018 zuwa yanzu, yawan matalauta dake cin gajiyar shirin ya kai sama da mutum miliyan 460, kana yawan kudin da aka yi tsimi don ba su jiyya ya kai kimanin kudin Sin Yuan biliyan 300.

Yayin da ake kusantar ranar tallafin matalauta karo na 7, wato ran 17 ga watan nan, Sin tana iyakacin kokari cimma burin samarwa dukkanin matalauta inshorar jiyya. Alkaluman da hukumar ba da tabbaci ga samar da jiyya ta bayar na nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2019, yawan matalauta da suka shiga inshorar jiyya ya dade a matsayin kashi 99.9%, kuma yawan kudin da aka karba daga gwamnati don kashewa a fannin inshorar jiyya mai tushe, da cututtuka masu tsanani, da ma tallafin jiyya ya kai kashi 80%.

Mataimakin shugaban hukumar Chen Jinpu ya ba da jawabi a dandalin, yana mai cewa, wadannan alkaluma sun bayyana rinjaye da Sin take da shi, a fannin ba da inshorar jiyya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China