Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Uganda ta samu karin kudaden shiga a rubi'i na farkon shekarar kasafin kudin 2020/2021
2020-10-14 11:06:52        cri
Hukumar haraji ta kasar Uganda ko URA a takaice, ta ce kasar ta samu karin kudaden shiga da yawansu ya kai sama da Shillings tiriliyan 1, kwatankwacin dalar Amurka 274, a rubu'i na farko na shekarar kasafin kudinta na shekarar 2020 zuwa 2021.

A shekarar kasafin kudin ta 2020 zuwa 2021, wadda ta fara daga ranar 1 ga watan Yuli, kasar ta samu ci gaban haraji a fannonin da suka hada da na saye da sayar da hajoji, da na sarrafa kayayyakin masana'antu, da fannin fasahar sadarwa, da hada hadar kudi da inshora, da kuma bangaren gudanarwar ayyukan al'umma.

URA ta ce, yayin da harajin watannin Afirilu da Mayu, da Yuni da Yuli ya ragu, kasar ta samu ci gaba a watannin Agusta da Satumba, wanda hakan ke nuni da yadda take farfadowa daga tasirin cutar COVID-19.

Hukumar harajin ta kuma yi hasashen samun harajin da yawansa ya kai Shillings tiriliyan 19.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 5.4 a zangon kasafin kudin na 2020 zuwa 2021, kasa da Shillings tiriliyan 20.3, wato kimanin dalar Amurka biliyan 5.6 da kasar ta samu a shekarar kasafin kudi ta 2019 zuwa 2020. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China