Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Covid-19: 'Yan kasar Uganda su 300 sun makale a kasar Sin
2020-04-14 15:30:04        cri

A ranar 12 ga watan Afirilun nan ne, jaridar "SUNDAY MONITOR" ta kasar Uganda, ta wallafa wani labari mai taken "Covid-19: Labarin 'yan kasar Uganda su 300 da suka makale a kasar Sin". Ga kuma abun da labarin ya kunsa:

A kalla 'yan kasar Uganda 300 ne suka makale a birnin kasuwanci na Guangzhou dake kasar Sin, yayin da ake tsaka da nuna kyamar baki, da tashin hankali, da nuna kyama, matakan da ke da nasaba da kin jinin 'yan Afirka a birnin, bisa zargin da ake yi cewa suna iya yada zagaye na biyu na cutar numfashi ta COVID-19.

A dukkanin nahiyar Asiya, birnin Guangzhou yanzu haka ya zamo birnin mafi karbar baki 'yan ci rani daga nahiyar Afirka da dama, musamman masu burin gudanar da hada-hadar cinikayya, ciki hadda wadanda ba su da cikakkun takardun yin hakan.

Cikin wannan mako, wannan kafar watsa labarai ta fitar da labari mai nasaba da kyamar baki 'yan Afirka, ciki hadda 'yan kasar Uganda, inda har wasu daka cikinsu ke cewa, an tursasa su yin gwajin lafiyar jiki, an fitar da su daga gidajen da suke haya, yayin da wasu ma suka ce an umarce su da ficewa daga inda suke zaune, alhali ba su da halin samun matsuguni.

To sai dai kuma, ita kanta wannan jarida ta zanta da wasu daga 'yan kasar ta Uganda dake zaune a birnin Guangzhou, da ma jami'an ofishin jakadancin kasar ta Uganda dake binrin Beijing, inda ta tabbatar da cewa, mafi yawan irin wadannan mutane suna zaune a birnin ne ba tare da ingantattun takardun shaida ba, inda wasu takarsunsu na visa suka kare, yayin da wasu ba su da cikakkun takardun da ake bukata.

A daya bangaren kuma, wani jami'in ofishin jakadancin kasar Uganda ya bayyana cewa, akwai 'yan kasar da dama dake zaune a boye, wadanda ba su da rajista, ko dai a ofishin jakadancin kasar su dake birnin Beijing, ko kuma a Guangzhou. Don haka suna tsoron zuwa a gwada lafiyar su, don gudun kar a gano matsalar dake tattare da takardun su.

Sai dai a gabar da ake tsaka da yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a birnin Wuhan, da ma wasu sassan lardin Hubei tsakanin watannin Disambar bara da Janairun wannan shekara, jami'in ya ce an matsa kaimi wajen yiwa mazauna gidaje gwajin lafiya na bai daya, ko da kuwa a ina mutum yake da zama.

Watanni 2 bayan hakan, kasar Sin ta kai ga shawo kan wannan cuta. Kaza lika hukumomi sun matsa kaimi wajen gudanar da bincike, da bukatar nuna takardun shaidar gwada lafiyar mutane, wanda hakan ne ya tsorata irin wadannan 'yan Afirka masu zaune ba tare da cikakkun takardu ba, da ma Sinawa masu gidajen da suke ba su mazauni.

Hakan ya kuma bankado Sinawa masu gidajen dake karbar kudin haya daga irin wadannan 'yan Afirka.

Abun da za a iya fahimta a nan a cewar jami'in shi ne, masu gidajen ba sa son 'yan sanda su san irin wadannan mutane na zaune a gidajensu. Don haka ne wasu ke ikirarin cewa an fitar da su daga gidajen da suke zaune, duba da cewa idan an kama irin wadannan Sinawa masu ba da hayar gidaje ba bisa ka'ida ba, suna iya fuskantar hukuncin dauri a gidan yari.

Kasar Sin Ta Bada Umarni

A ranar 5 ga watan Afrilu, ofishin kula da harkokin waje na gwamnatin birnin Guanzhou, ya bayar da wata sanarwar dake umartar dukkan baki su gabatar da bayanansu na lafiya, wanda galibin 'yan Afrika ba su da shi.

An rubuta sanarwar ne kamar haka, "akwai bukatar ku samu lambar Yuekang da lambar Suikang dake kan karamar manhajar. Za ku bukaci gabatar da lambobin Yekang da na Suikang a lokacin da kuke shiga ko fita daga wasu wurare, kamar rukunin gidaje da otel da shagunan sayayya.

Idan ba a muku gwajin cutar SARS da CoV-2 ba bayan shiga kasar Sin, sai ku je a muku gwajin da ake daukar samfuri daga makogwaro da na kwayoyin jini, wadanda duka kyauta ne. Za ku iya tuntubar kwamitocin unguwarku."

A sakamakon haka, aka bukaci dukkan mazauna ciki har da baki, su yi gwajin na tilas, wanda jami'in ya ce galibin 'yan Afrika na fargaba.

Bisa la'akari da yadda cutar COVID-19 ke bazuwa a wajen kasar Sin, ana dar-dar da baki, ciki har da 'yan Afrika. Sai dai akwai yiwuwar yadda galibin 'yan Afrika suka shiga dandalin sada zumunta suna bayyana damuwarsu, ya fusata hukumomin kasar Sin dake Beijing, wadanda suka yi yaki da annobar ta hanyar sa ido kan yaduwar bayanai.

"Kuma dama a irin wadannan yanayi, jami'an diflomasiyyar Afrika kan ja kafa wajen daukar mataki saboda sun san cewa yawancin mutanen da batun ya shafa sun keta doka," cewar wani jami'in diflomasiyya a Kampala.

Yayin da ofishin jakadancin kasar dake Beijin ke daukar matakan da suka kamata, Sunday Monitor ta gano cewa, akwai wata matsala, saboda jakadan Uganda a kasar Sin, Dr. Crispus Kiyonga na gida Uganda, tun cikin watan Disamban bara.

Wasu daga cikin 'yan kasar Uganda da jaridar ta tattauna da su, sun ce suna son a kwashe su zuwa gida, suna masu bada dalilan matsanancin yanayin zaman rayuwa da suka yi ikirarin na da nasaba da matsalolin tattalin arziki.

A birnin Kampala, babban sakataren ma'aikatar harkokin wajen kasar, Mr Patrick Mugoya, ya shaidawa jaridar a farkon makon nan cewa, a yanzu, babu wani shiri da ake da shi na kwashe 'yan kasar dake ketare.

Ganawar Jami'an Diflomasiyya

Ministan harkokin wajen kasar, Sam Kutesa ya gana da Jakadan kasar Sin dake Uganda Zheng Zhuqiang dangane da yanayin da 'yan kasar ke ciki a kasar Sin.

Ministan ya bayyana matsananciyar damuwar gwamnatin kasar kan yadda ake cin zarafin jama'arsu. Ya yi kira ga gwamnatin kasar Sin ta gaggauta shiga tsakani don magance matsalar da 'yan Uganda ke fuskanta a kasar Sin.

Jakadan ya tabbatarwa Ministan cewa, kasar Sin na girmama dangantakarta da Uganda da kuma sauran kasashen Afrika.

Ya ce gwamnatin Sin na daukar matakan da suka dace na magance matsalar tare da gabatar da kofarin gwamnatin Uganda ga hukumomin da suka dace a kasar Sin. (Saminu Alhassan & Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China