Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya ya samar da dala miliyan 148 domin inganta gandun daji a Uganda
2020-04-28 12:04:36        cri
Bankin duniya ya samar da kudade da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 148, domin aikin inganta gandun daji, da kare yankunan bude ido a kasar Uganda.

Wata sanarwar da bankin ya fitar a jiya Litinin, ta nuna cewa, bankin ya tanaji rancen kudi har dala miliyan 78.2 ga kasar, da kuma tallafin dala miliyan 70, kudin da cikin su za a ware dala miliyan 58 ga aikin kyautata rayuwar 'yan gudun hijira, da al'ummun dake wuraren da aikin zai shafa.

An tsara kashe kudin ne a yankin Albertine, da kuma yankunan matsugunan 'yan gudun hijira dake arewa da yammcin kasar ta Uganda.

Babban bankin duniya dai ya ce yankin Albertine, shi ne cibiyar hada hadar yawon bude ido a kasar, wanda ke samar da babbar gudummawa ga tattalin arzikin kasar a fannin kudaden musaya, da guraben ayyukan yi ga 'yan kasar.

Ana fatan shigar da makudan kudaden cikin aikin shuke gandun daji, da itatuwan katako domin samar da riba, matakin da ake fatan zai zama wata dama ta mayar da fannin, wani jigon tattalin arziki mai zaman kan sa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China