Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira da a fito da tsarin tabbatar da tsaron alkalumai a duniya
2020-10-13 20:59:11        cri

Yau kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba shiryawa a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta yi kira ga bangarori daban daban da su goyi bayan shawarar tabbatar da tsaron alkaluman duniya ta hanyar tsara ka'idar da za a bi, ta yadda za a kiyaye tsaron yanar gizo a fadin duniya.

Rahotanni da kafofin watsa labaran ketare suka gabatar, na nuna cewa, kungiyar Five Eyes da kasashen Japan da Indiya sun bukaci kamfanonin kimiyya da fasaha kamar Signal da Telegram da su ba hukumomin shari'a damar duba alkaluman manhajarsu, ta yadda za su sa ido kan laifuffuka ta yanar gizo.

Kan wannan batun, Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, kasashe mambobin kungiyar Five Eyes sun dade suna zargi kamfanonin kasar Sin ba gaira ba dalili wai suna zama barazana ga masu amfani da kayayyakinsu ta manhajarsu, amma yanzu kungiyar ta bukaci kamfanonin da su samar da damar karanta alkaluman manhajarsu, ko suna amfani da ma'auni iri biyu ne?

Jami'in ya kara da cewa, kwanan baya, kasar Sin ta gabatar da shawarar tabbatar da tsaron muhimman bayanai na duniya, inda ta yi kira ga kamfanonin sadarwa cewa, kada su ba da damar karanta bayanai a kayayyakinsu ko hidimominsu, idan akwai bukata, ya dace hukumomin shari'a su tattauna da bangarorin da abin ya shafa domin daidaita lamarin bisa doka.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China