Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 8 da yan bindiga suka hallaka a arewacin Najeriya
2020-10-13 10:13:32        cri
Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 8 wadanda 'yan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai a wani kauyen dake jihar Katsina a shiyyar arewa maso yammacin kasar.

An kai harin ne da yammacin ranar Lahadi a kauyen Shau dake karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, kakakin hukumar 'yan sandan jihar Gambo Isah, ya tabbatar da harin.

Isah ya ce, maharan sun kone gidaje masu yawa inda ba a san hakikanin manufar su na kaddamar da harin ba.

Jami'in 'yan sanda ya ce, ma'aikatansu suna cigaba da bincika dukkan yankunan domin binciko 'yan bindigar wadanda suka tsere bayan sun kaddamar da mummunan harin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China