Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Likitoci biyu da aka yi garkuwa da su a Najeriya sun kubuta
2020-10-12 09:46:07        cri
'Yan sanda a jahar Kogi dake arewa ta tsakiyar Najeriya sun ce sun yi nasarar kubutar da likitoci biyun da aka yi garkuwa da su a wasu sassan jahar.

Kakakin 'yan sandan jahar, William Aya, wanda ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho, ya ce, Ejike Mgbeahurike, likita ne wanda aka yi garkuwa da shi a asibitinsa mai zaman kansa dake yankin Ayingba a ranar Laraba, an ceto shi a wani daji dake kan hanyar Ayingba-Ankpa a safiyar ranar Lahadi.

Ya kara da cewa, likita na biyu shi ne Yahaya Ebiloma, wanda aka yi garkuwa da shi a garin Ankpa a ranar Talata, shi ma an yi nasarar kubutar da shi daga hannun masu garkuwar.

A ranar Juma'ar da ta gabata, kungiyar likitoci ta Najeriya ta bayyana rashin jin dadinta game da garkuwa da mambobinta biyu, inda ta bukaci 'yan sanda da gwamnatin kasar su yi bakin kokarinsu don ganin an kubutar da su.

Yin garkuwa da baki 'yan kasashen waje da fitattun mutane na cigaba da karuwa a Najeriya a baya bayan nan.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China