Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mukaddashin wakilin Sin dake Najeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar
2020-10-10 15:30:42        cri

Mukaddashin wakilin Sin dake Najeriya Zhao Yong, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama, jiya Juma'a.

A ganawar tasu, Zhao ya nuna cewa, Sin da Najeriya abokan juna ne kuma aminai. Ya ce a watan Fabrairun badi, za a cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, inda ya ce Sin na fatan kara hadin kai da Najeriya don tabbatar da ci gaban da shugabannin kasashen biyu suka samu yayin taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika da ma taron musamman na yakar COVID-19 tare, ta yadda za su kara hadin kai a fannoni daban-daban, da amfanawa jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangare, Geoffrey Onyeama ya ce, Najeriya da Sin na da dangantakar kut da kut, kuma kasarsa na mai da hankali matuka kan rawar da Sin take takawa kan harkokin kasa da kasa, yana mai fatan kara hadin kai da Sin a fannoni daban-daban, da ingiza dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China