2020-10-10 15:29:39 cri |
Bayanin ya nuna cewa, sharhin da mai nazarin manufofin Afrika da gabas ta tsakiya na asusun ba da lamuni na Amurka ya bayar mai taken "Mai yiwuwa kasar Sin na leken asiri kan gine-ginen gwamnatin Afrika" ba shi da wani shaida ko kadan.
Bayanin ya ce, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taba bayyana cewa, ba wata kasa da take taimakawa Najeriya tun bayan da ta samu 'yancin kai kamar Sin. Shi ma a nasa bangare, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, ba wanda zai lahanta hadin kan jama'ar bangarorin biyu.
Bayanin ya kara cewa, Sin tana baiwa nahiyar tallafin jin kai ba tare da wani sharadi ba, kuma tana iyakacin kokarin taimakawa nahiyar wajen yaki da cutar Ebola da COVID-19. Ya ce kasashen Afrika na zaba hanyar da za su bi, wato hada hannu da kasar Sin, da ma ci gaba da raya dangantakar bangarorin biyu duk da ganin sauyawar halayen kasa da kasa. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China