Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Afrika sun hada hannu domin yaki da annobar COVID-19
2020-06-17 10:51:46        cri

Yayin da cutar COVID-19 ke kara bazuwa a duniya, yanayin yaduwar cutar a nahiyar Afrika na kara muni. A matsayinta na babbar kasa mai sauke nauyin dake wuyanta, kasar Sin ta wuce gaba wajen taimakawa nahiyar magance bukatunta na gaggawa.

Galibin kasashe da hukumomin nahiyar Afrika, sun samar da taimako mai muhimmanci ga kasar Sin a lokacin da take cikin mawuyacin hali na yaki da COVID-19.

Cikin 'yan kwanakin da suka gabata, shugabannin Afrika da dama sun bayyana godiyarsu ga kasar Sin a lokuta da dama, suna cewa, hadin gwiwarsu a yaki da annobar COVID-19 na bayyana muhimmancin gina al'umma mai makoma ta bai daya ga bil adama.

Da yake bayyana godiyarsa ga kasar Sin, shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe, ya ce tallafin da take ci gaba da bayarwa, na nuna muhimmancin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen 2. Yana mai cewa irin taimakon da take bayarwa zai taimakawa kasashen nahiyar yakar COVID-19.

A bana, dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika ke cika shekaru 20. Yayin da ake fuskantar kalubalen COVID-19, kasar Sin da Afrika za su iya daukar darasi daga hadin gwiwa da goyon bayan juna.

Wata mai bincike ta cibiyar nazarin Afrika ta kasar Sin He Wenping ta ce, a nan gaba, ya kamata bangarorin biyu su kara karfafa hadin gwiwarsu a bangaren tsarin kiwon lafiyar al'umma.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China