Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya bukaci a karfafa yaki da ta'addanci a yammacin Afrika da yankin Sahel
2020-01-09 09:43:23        cri

Wakilin kasar Sin a MDD ya bukaci kasa da kasa su kara kaimi wajen yaki da barazanar ta'addanci a yammacin Afrika da yankin Sahel, wanda ya hada da daukar matakan tallafawa kasashen dake shiyyar wajen bunkasa karfin shiyyar.

A lokacin taron kwamitin sulhun MDD game da shiyyar, Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya ce akwai bukatar kasa da kasa su tallafawa kasashen dake shiyyar wajen samun kwarin gwiwar yaki da ayyukan ta'addanci da yaki da tsattsauran ra'ayi.

Game da irin kokarin da kasar Sin ke yi a wannan fanni, Wu ya bayyana cewa kasar Sin ta kafa wani asusu don samar da tallafi ga shirin hadin gwiwar Sin da Afrika a fannin aikin wanzar da zaman lafiya da tsaro da kuma samar da dawwamamman zaman lafiyar shiyyar.

Ya ce kashin farko na kayan tallafin wanda Sin ta aika ya tasamma RMB miliyan 200 kwatankwacin dala miliyan 28.8 ya riga isa Afrika don tallafawa ci gaban rundunar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta ko-ta-kwana ta Afrika don bayar da daukin gaggawa yayin da aka fuskanci rikici.

Bugu da kari, wakilin Sin ya ce kasarsa ta samar da RMB miliyan 300 kwatankwacin dala miliyan 43.2 wajen taimakawa ayyukan yaki da ta'addanci a yankin Sahel da bunkasa ci gaban rundunar hadin gwiwar wanzar da tsaro ta kasashe biyar na yankin Sahel.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China