Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya yi kira ga kasashen duniya da su kara zage damtse wajen yaki da talauci
2020-10-12 20:05:14        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga kasashen duniya, gami da jam'iyyun siyasu a dukkan kasashe, da su hada kai, wajen hanzarta kokarin da ake yi na yaki da talauci a duniya, duba da irin matsaloli da kalubale da ake ci gaba da fuskanta a wannan fanni.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS, ya yi wannan kiran ne Litinin din nan, cikin sakon taya murna da ya aikawa taron karawa juna na kasa da kasa game da yaki da talauci da nauyin dake bisa wuyan jam'iyyun siyasu, wanda aka bude a Fuzhou, babban birnin lardin Fujian dake gabashin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China