Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya bukaci jami'ai matasa su mayar da hankali kan warware kalubaloli na zahiri
2020-10-11 16:25:34        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci jami'ai matasa su kara sa himma da kwazo wajen kokarin warware dukkan matsalolin da ake cin karo da su na zahiri, ya kamata a sa kaimi, kuma a samar da hakikanin sakamako, in ji shugaban na Sin.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na jami'iyyar kwaminis, kana shugaban kwamitin aikin sojin kasar, ya yi wannan kira ne a lokacin bude kwas din horas da matasan jami'ai da masu matsakaitan shekaru a kwalejin horas da 'yan jami'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC.

Tarihi ya samu ci gaba ta hanyar warware matsaloli, Xi ya jaddada cewa, ta hanyar jagorantar al'umma don samar da juyin juya hali, da gina kasa, da sauye sauye, kuma baki daya manufar jami'iyyar ita ce warware dukkan matsaloli na zahiri a cikin kasa.

A wannan hali da ake ciki mai cike da sarkakiya, da wahalar sha'ani, Xi ya ce, akwai bukatar gaggawa ga jami'ai su kara karfafa matakansu na warware matsaloli, ya kara da cewa, bukata ce wadda ta zama tilas ga jami'ai matasa su samu kwarin gwiwa.

Xi ya ce, jami'ai, musamman matasa, tilas ne su kara himma kan muhimman ayyukan al'umma dake bisa wuyansu, kuma su yi amfani da dukkan karfinsu wajen nazartar al'amurra, da zartar da hukunci bisa tsari na hikima, da zurfafa yin gyare gyare, da daukar matakai na gaggawa, da tattaunawa tare da jama'a, da kuma aiwatar da manufofi yadda ya kamata.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China