Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya aike da sakon taya murnar cika shekaru 75 da kafuwar Jam'iyyar WPK ta Koriya ta arewa
2020-10-10 17:36:07        cri
Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban kasar, Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga Kim Jong Un, shugaban jam'iyyar kwadago ta WPK ta Koriya ta arewa, bisa cikar jam'iyyar shekaru 75 da kafuwa.

A cewar shugaba Xi, har kullum, a shirye Sin take ta hada hannu da Koriya ta arewa wajen raya dangantakar dake tsakaninsu, da ingiza ci gaban manufofin gurguzu na kasashen biyu, domin kara samar da moriya ga kasashen da al'ummominsu da kuma bayar da sabuwar gudunmuwa ga zaman lafiya da tsaro da ci gaban yankinsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China