Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Huldar dake tsakanin Sin da Afirka a idon Xi Jinping
2020-10-12 16:33:59        cri

 

 

A yau Litinin, an samu cika shekaru 20 da kafuwar dandadin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC). Bisa kokarin karfafa hadin kai da kasashen Afirka da kasar Sin suka yi, dandalin FOCAC ya riga ya zama wani tsari mai amfani domin bangarorin Sin da Afirka su tattauna matakan da za a iya dauka don karfafa zumunta da hadin gwiwa a tsakaninsu. A nan za mu maimaita wasu maganganun da shugaba Xi Jinping ya taba fada dangane da huldar dake tsakanin Sin da Afirka.

A wajen wani taron koli da aka kira a watan Yunin bana, don tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, a kokarin tinkarar cutar COVID-19, shugaba Xi na kasar Sin ya ce, "Kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka a kokarinsu na dakile cutar COVID-19, don cika alkawarin da na yi a wajen bikin kaddamar da taron kungiyar lafiya ta duniya WHO. " Ban da wannan kuma, ya ce, "Duk wani yanayin da duniyar mu ke ciki, kasar Sin ba za ta canza niyyarta ta karfafa hadin kai tare da kasashen Afirka ba."

 

Sa'an nan, a wajen bikin kaddamar da taron koli na dandalin FOCAC da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin a watan Satumban shekarar 2013, shugaba Xi Jinping ya ce, "Kasar Sin na son ganin kasashen Afirka sun samu ci gaba cikin sauri tare da kasar Sin. Ba wanda zai iya hana jama'ar Sin da Afirka raya al'ummunsu!" (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China