Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ga yadda manoman yankunan tsaunuka dake lardin Hubei suke kyautata rayuwarsu ta hanyar jawo masu bude ido
2020-09-24 19:47:27        cri
Yayin wata ganawa da wani dan jarida, Liu Mingjian mazauni kauyen Yuanheguan dake lardin Hubei ya bayyana cewa, "A baya, nan ba komai sai gidajen da suka rushe, amma yanzu kauyawan wurin na sayen hannun jari na gidaje, kuma matalauta magidanta suna mallakar gidaje, tare da shiga harkar ba da hidima a fannin yawon bude ido." Liu Mingjian ya ce "Kalli yadda irin wadannan muhallai suke, ga kuma 'yan yawon shakatawa na ta daukar hotuna.

A yunkurinta na samar da riba daga albarkatun yawon bude ido, ta yadda hakan zai bunkasa tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'umma, hukumar Wudangshan mai lura da yankin tattalin arziki na musamman a lardin na Hubei, a 'yan shekarun nan, ta aiwatar da wasu tsare-tsare na inganta harkar yawon bude ido, ta yi wa gidajen mazauna kauyukan dake kewayen wurin har 33 gyaran fuska, kana ta mayar da su masaukan baki. Kamar dai yadda Liu Mingjian ya tabbatar da hakan, bayan da shi kansa ya ci gajiya daga wannan shiri.

A daya hannun kuma, akwai wani babban sauyi da ya wakana a yankin hakar ma'adanai na Huangshi, wanda ke kudu maso gabashin lardin na Hubei. Tsaye gaban "Rami na lambawan a Asiya", a ko ina, ana iya ganin korayen tsairrai. Abu ne mai wahala mutum ya iya zaton cewa nan wuri ne da a baya, aka taba hakar ma'adanai a cikin sa, inda a lokacin tsirrai ba sa iya fitowa, kuma cike yake da ramuka.

Domin dawowa kyakkyawan yanayin halittu, da nacewa manufar ci gaba da kare muhalli, birnin Huangshi ya sauya yanayin wannan wuri zuwa wani lambun shakatawa, an shuke shi da itatuwa, duk da tarin duwatsu da ramukan mahakar ma'adanai dake wurin. Kaza lika an inganta yanayin shuke shuken, da yanayin karkashin kasar wurin, zuwa lambu mai ban sha'awa. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China