Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a shirya bikin murnar cika shekaru 40 da kafuwar yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen
2020-10-12 10:33:53        cri
Za a gudanar da bikin cika shekaru 40 da kafuwar yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen wanda zai gudana a birnin dake lardin Guangdong a ranar Laraba 14 ga watan Oktoba, inda shugaban kolin kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin kuma zai gabatar da muhimmin jawabi.

A lokacin bikin, babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin CMG, da kafar yada labarai ta Xinhuanet.com, za su watsa shirin kai tsaye, kana manyan shafukan watsa labarai ta intanet na kasar Sin da suka hada da People.com.cn, CCTV.cn da China.org.cn, za su dinga watsa labaran domin bayyana abubuwan dake wakana ga dandalin yada labarai na zamani da suka hada da app na People's Daily, da na Xinhua News da na CCTV News. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China