Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Jamus: Babu Wanda Zai Maye Gurbin Shenzhen
2020-08-27 15:16:37        cri

A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, Shenzhen ya bunkasa zuwa birni na zamani daga matsayin dan karamin kauye na masunta, abin da ya jawo hankalin kasashen duniya. Al'adun kirkire-kirkire ya karawa wannan yanki kuzari matuka, matakin da ya jawo kamfanonin kasashen duniya da dama.

Kafa cibiyoyin bincike kirkire-kirkire a Shenzhen, shi ne burin kamfanoni masu jarin ketare da dama. A ranar 30 ga watan Yuli, an kafa cibiyar kirkire-kirkire ta kungiyar masu masana'antun kasar Jamus a birnin, cibiyar da ta kasance ta farko da kungiyar 'yan kasuwar Jamus dake kasa da kasa ta kafa a duniya. Babban wakilin reshen Guangzhou na kungiyar kana shugaban zartaswa na kungiyar 'yan kasuwa ta Jamus na yankin kudanci da kudu maso yammacin kasar Sin Ma Mingbo ya shedawa manema labarai na CMG cewa, yadda birnin Shenzhen ke bude kofarta da yin hakuri da bangarori daban-daban shi ne abin da ya burge shi, yanayi mai kyau na kirkire-kirkire da yankin yake da shi ya sa Ma Mingbo ya yanke shawarar fara sha'aninsa da ma tsayawa a birnin.

An yiwa Shenzhen lakabi da "Silicon valley na kasar Sin", amma a ganin Ma, ba wanda zai iya maye gurbin yankin, wanda ya kasance cibiyar kirkire-kirkire a fannin na'urori

A cewarsa, aikin kirkire-kirkire ya fi jawo hankalinsu, akwai sauran yankunan da suka shafi kirkire-kirkire a sassan daban-daban a duniya, amma Shenzhen ya bambanta, wato yana da wani yanayi mai muhimmanci kirkire-kirkire wajen raya harkokin da suka shafi na'urori, inda suke iya samun fasahohi da kimiyya na zamani, da kuma neman kwararru a wannan fanni, saboda haka, a ganinsa, Shenzhen wuri ne dake da boyayyen karfi a fannin kirkire-kirkire.

Ko da yake, cutar COVID-19 ta dabaibaye duniya baki daya, ta kuma kawo babbar illa ga sana'o'i daban-daban. Wasu kamfanoni masu fitar da kayayyaki zuwa ketare suna fuskantar kalubaloli da dama, amma kamfanonin Jamus sun yanke shawarar ci gaba da gudanar da ayyukansu a nan kasar Sin.

Ma Mingbo ya ce, kungiyar 'yan kasuwar Jamus dake kasar Sin, ba ta samu sakwannin barin kasar Sin ba daga kamfanonin Jamus. Sin muhimmiyar abokiyar ciniki ce ta kasar Jamus, kamfanonin Jamus na matukar sha'awar ci gaba da zuba jari a kasar Sin. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China