Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasahar 5G ta karade birnin Shanzhen baki daya
2020-08-18 21:13:58        cri
Magajin garin Shenzhen Chen Rugui ya sanar a jiya Litinin cewa, yanzu haka ana amfani da fasahar 5G a birnin baki daya.

Shi ma darektan kwamitin kula da harkokin masana'antu da fasahar sadarwa na birnin Shenzhen Jia Xingdong, ya bayyana cewa, yawan tashoshin 5G a birnin na Shenzhen, sun haura 46,000, adadin da ya zarce wanda birnin ya tsara kafawa.

Birnin Shenzhen dake lardin Guangdong na kudancin kasar Sin, cibiya ce ta rukunin kamfanonin kasar dake sahun gaba gami da manyan kamfanonin fasaha, ciki har da Huawei da Tencent.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China