Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta mayar da Shenzhen yankin gwaji mai halayyar gurguzu ta musamman
2019-08-19 10:01:46        cri

Wasu takardun bayanai da kwamitin kolin JKS, da majalissar gudanarwar kasar suka fitar, sun nuna cewa, za a gina birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin, ta yadda zai zama yankin gwaji na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin mai matukar kayatarwa.

Takardun bayanan wadanda aka fitar a jiya Lahadi, sun nuna cewa, gina wannan yanki zai taimaka wajen kara aiwatar da manufofin zurfafa gyare gyare, da kara bude kofa ga waje daga dukkanin fannoni.

Aikin zai kuma tallafa wajen cimma nasarar aiwatar da manufar gina yankin Guangdong zuwa Hong Kong zuwa Macao, tare da alamta cimma burin kasar Sin na zama kasa wadda ke farfadowa.

Takardun bayanan sun kara da cewa, nan da shekarar 2025, Shenzhen zai zama daya daga manyan birane a duniya a fannin bunkasar tattalin arziki da ingancin ci gaba. Kaza lika tsarin birnin na bincike da bunkasuwa, da nagartar masana'antu, da fadadar kirkire kirkiren sa, tare da kyautatar hidimomin al'umma, da ma kyakkyawan yanayin muhallin halittun birnin, duka za su zamo a sahun gaba a duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China