Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe yan bindiga 5 a sintirin hadin gwiwa a kudancin Somalia
2020-10-11 17:02:37        cri

Rundunar sojojin kasar Somalia SNA wacce ke samun goyon bayan dakarun jihar Kudu maso yamma ta yi nasarar kashe mayakan al-Shabab 5 a ranar Asabar a wani aikin sintiri na hadin gwiwa da suka gudanar a garin Dinsor, dake shiyyar kudancin kasar.

Dakarun hadin gwiwar sun kaddamar da hare hare a sansanonin dake karkashin ikon 'yan ta'adda a garin, bayan samun korafe korafe daga mazauna yankin, a cewar Shine Mayow, kwamandan rundunar tsaro ta jihar Kudu maso yamma a garin Dinsor.

Mayow ya ce, 'yan ta'addan sun killace mazauna garin Dinsor, sun kuma datse dukkan wasu hanyoyin shiga garin. Daga bisani jami'an tsaron sun gudanar da aikin sintirin tare da taimakon mazauna garin. Sun kashe 'yan bindigar 5 a lokacin musayar wuta tsakanin sojojin da 'yan ta'addan masu tsattsauran ra'ayi.

Ya kara da cewa, sojojin sun yi nasarar fatattakar 'yan bindigar daga garin.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China