Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani jirgi ya fadi a filin jirgin saman Somalia, sai dai, babu asarar rai
2020-07-15 10:21:02        cri

Wani jirgin da ya taso daga kasar Djibouti dauke da kayayyakin abinci na tallafi, ya fadi jiya, lokacin da yake sauka a filin jirgin saman Ugaas Khalif na garin Beledweyne dake yankin Hiiraan na tsakiyar Somalia.

Abdirahman Riyale, kwamandan runduna ta 4, ta rundunar sojin Djibouti dake karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya na AU, ya shaidawa manema labarai a filin jirgin saman cewa, an ceto mutane 3 dake cikin jirgin, yayin da kayayyakin abincin suka kone.

Ya ce abincin tallafi ne daga gwamnatin Djibouti, zuwa ga fararen hular da ambaliyar ruwa a yankin tsakiyar Somalia ta shafa.

Kakakin rundunar AU dake Somalia AMISOM, Charles Imbiakha, ya ce nan bada dadewa ba, za a kaddamar da bincike domin gano musababbin hadarin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China