Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya bukaci bangarorin Somalia su hada kai don ciyar da tsarin siyasar kasar gaba
2020-05-22 09:30:55        cri

Yao Shaojun, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bukaci bangarori daban daban na kasar Somalia su yi aiki tare da juna domin samun nasarar gudanar da zaben kasar cikin kwanciyar hankali da bunkasa ci gaban harkokin siyasar kasar.

Yao ya ce Somalia tana cikin wani muhimmin lokaci, kasancewar batun zaben kasar shi ne aka baiwa fifiko a halin yanzu.

Shugaban kasar Somalia ya rattaba hannu kan dokar zaben kasar. Kwamitin tsara zabukan kasar ya gabatar da daftari na jadawalin zaben kasar, kana ya yiwa daftarin gyare gyare domin yin rajistar masu zabe.

Yao, ya fadawa kwamitin sulhun MDD cewa, wannan ci gaba da aka samu ya nuna yadda kasar Somalia ta sha alwashin gudanar da ingantaccen zabe cikin kwanciyar hankali. Kasar Sin tana goyon bayan dukkan bangarorin kasar Somalia domin sauke muhimmin nauyin dake wuyan kasar, da bunkasa hadin gwiwa da tattaunawar sulhu, da kuma yin hadin gwiwa da nufin inganta batun zabe da tsarin siyasar kasar.

A cewar wakilin na Sin, ya kamata kasa da kasa su samar da cikakken taimako tare da nuna karamci ga tsarin shugabancin kasar Somalia. Kasar Sin tana nacewa kan matsayinta inda ta bukaci kasashen Afrika su warware matsalolin dake shafar Afrika bisa tsarin da ya dace da yanayin Afrika.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China