Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Somalia sun halaka mayakan al-Shabab 9 a kudancin kasar
2020-05-08 10:17:29        cri
Sojojin kasar Somalia, sun kashe mayakan al-Shabab 9, yayin wata arangamar da aka yi tsakaninsu, jiya a yankin Lower Shabelle.

Kwamandan rundunar sojin Somalia, Abdi Hamid Mohamed Dirir, ya shaidawa manema labarai cewa, mayakan al-Shabab sun kaddamar da hari kan sansanin soji dake Awdhigle, amma sai sojoji suka dakile yunkurinsu.

Abdi Dirir, ya ce dakarun rundunar na cikin shirin ko-ta-kwana a ko da yaushe, abun da ya kai su ga gano yunkurin mayakan kan sansanin. Ya ce baya ga kashe mayakan al-Shabab 9, sojojin sun kuma kwato makamai daga wajen su.

Lamarin na baya-bayan nan, ya auku ne kwanaki 2, bayan dakarun gwamnati sun kashe mayakan al-Shabab 6, yayin wata arangama a garin Qoryoley, wanda shi ma ke yankin kudancin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China