Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya yi wa Trump da Melania fatan samun sauki
2020-10-03 20:23:26        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi wa takwaransa na Amurka Donald Trump da Mai dakinsa Melania, fatan samun sauki cikin gaggawa.

A sakon nasa, Xi ya ce bisa la'akari da jin cewa shugaba Trump da mai dakinsa Melania sun harbu da cutar COVID-19, shi da uwargidansa Peng Liyuan, suna jajanta musu tare da musu fatan samun lafiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China