Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping da iyalansa
2020-10-01 20:47:40        cri
Yau 1 ga wata rana ce ta cika shekaru 71 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, kuma a wannan shekara ce, bikin gargajiyar Sinawa da ake kira Zhongqiu ya fado a daidai wannan rana, bikin da al'ummar Sinawa kan gudanar a ranar 15 ga wata na takwas bisa kalandar gargajiya, inda suke haduwa da iyalai tare da kallon wata da cin wainar wata da kuma murnar samun girbi mai armashi da fatan samun alheri. To a daidai wannan lokacin da al'ummar Sinawa ke murnar wannan muhimmiyar rana, sai a sha labarin shugaban kasar Sin Xi Jinping da iyalansa.

Xi Zhongxun shi ne mahaifin Xi Jinping, kuma ya taba zama jagora a lardin Guangdong da ke kudu maso gabashin kasar Sin. Malam Xi Zhongxun ya ce, "Duk abin da zai amfana wa al'umma da kuma kasa, to, za mu yi, kuma ba tare da jin tsoro ba."

Abin da Xi Jinping ya yi ke nan. Bayan da ya hau karagar mulkin kasar Sin a shekarar 2012, a jawabin da ya gabatar ya bayyana cewa, "burin jama'a na yin rayuwa mai dadi shi ne burin da muke kokarin neman cimmawa."

Shugaba Xi Jinping kusan ya ziyarci dukkanin sassan da ke matukar fama da talauci a kasar Sin. Tun bayan shekarar 2013, sama da mutane miliyan 10 ne suke fita daga kangin talauci a kowace shekara, matakin da ya ba da gudummawar da ta kai sama da 70% ga aikin saukaka fatara a fadin duniya. A bana kuma, shugaba Xi Jinping ya sha jaddada cewa, ya zama dole a hada karfi da karfe don cimma nasarar yaki da talauci, duk da munanan illolin da annobar COVID-19 ke haifarwa, ta yadda za a cimma burin da aka sanya gaba na saukaka fatara da gina al'umma mai matsakaicin wadata.

A lokacin da shugaba Xi Jinping yake karami, mahaifiyarsa ta kan ba shi labarin marigayi Yue Fei, wani babban jarumi da ya bauta wa al'umma da kuma sadaukar da ransa ga kasarsu.

Bayan da Xi Jinping ya kama aikin shugabanci, mahaifiyarsa ta sha rubuta masa wasika, inda ta bukace shi da ya bi ka'ida, ta kuma kira taro a gida, inda ta bukaci sauran 'ya'yanta da kada su gudanar da kasuwanci a fannonin da Xi Jinping ke aiki.

A yayin da Mr.Xi Jinping ke rike da kujerar babban sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na lardin Zhejiang, a zantawarsa da 'yan jarida, ya ce, "Kowace rana ina yin waya da uwargidana, shekaru sama da 10 da aurenmu."

Bayan da ya zama shugaban kasar Sin, uwargidansa Madam Peng Liyuan ta yi ta tallafa masa a harkokin tafiyar da kasa, tare da bayyana wa duniya irin al'adar Sinawa na dora muhimmanci a kan iyali.

Iyalai su ne tushen kasa, kuma burin shugaban kasa shi ne al'ummarsa su ji dadin rayuwa tare da iyalansu. Shugaba Xi Jinping ya kuma cusa irin wannan ra'ayi na dora muhimmanci a kan iyali da kuma tarbiyyar iyali cikin aikinsa na tafiyar da harkokin kasa. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China