Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Zambiya: FOCAC na da muhimminci wajen karfafa hadin gwiwa
2020-10-11 16:10:23        cri

Wani babban jami'in gwamnatin kasar Zambiya ya ce, kasarsa tana matukar dora muhimmanci kan dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC, a matsayin wani muhimmin dandalin karfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa da kuma bunkasa ci gabansu.

Chalwe Lombe, babban sakatare a ma'aikatar harkokin waje da hulda da kasa da kasa na Zambiya, ya ce an cimma nasarori masu yawan gaske tun bayan kafa dandalin FOCAC shekaru 20 da suka shude, kuma a cewar jami'in, ana fatan hadin gwiwar dake tsakanin Zambiya da Sin za ta ci gaba da kara karfafuwa.

Ya kara da cewa, jarin da Sin ta zuba wajen gina ababen more rayuwa a kasar Zambiya sun kara ba da kwarin gwiwa a fannin hada hadar kudin kasar ta Zambiya, sun samar da karuwar arziki da damammakin guraben ayyukan yi a fannoni da dama da suka hada da fannin hakar ma'adanai, lamarin da ya haifarwa kasar samun karuwar fitar da ma'adanin jan karfe zuwa kasashen ketare.

Lombe ya kara da cewa, aikin gina babban dakin taro na zamani a birnin Lusaka yayin da kasar Zambiya ke shirin karbar bakuncin babban taron kolin AU a shekarar 2022, da kuma kafa manyan cibiyoyin bunkasa tattalin arziki guda biyu, wadanda suka samar da damammakin guraben aiki ga mutanen kasar manyan nasarori ne.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China