Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tashar samar da lantarki mai amfani da hasken rana da kamfanin Sin ya gina a Zambiya ta soma aiki
2019-12-22 16:21:19        cri

Jiya Asabar, aka shirya bikin fara amfani da tashar samar da lantarki mai amfani da hasken rana wanda kamfanin Huawei na kasar Sin ya tallafawa yankin Chibwika dake jihar North-Western ta kasar Zambiya. A yayin bikin, shugaban kasar Edgar C. Lungu ya bayyana cewa, tashar za ta biya bukatun mazauna wurin wajen samun damar amfani da lantarki, hakan zai kyautata zaman rayuwar mutanen sosai.

Baya ga haka, shugaban ya yi godiya ga kamfanin Sin da ya nuna goyon baya ga ci gaban al'ummar kasarsa. A cewarsa, Zambiya tana da dunbun albarkatun makamashin hasken rana, amma ba ta amfani da su yadda ya kamata, don haka dole ne gwamnatin kasar ta maida hankali wajen bunkasa fasahar makamashin hasken rana.

Shugaban ya kara da cewa, tashar za ta samar da wutar lantarki ga gidaje 300 da makarantu da kuma cibiyoyin samar da jinya da dai sauransu na wurin, wadda zata kyautata zaman rayuwar jama'ar wurin, da taimaka musu wajen gudanar da ayyuka, hakan zai bayar da gudumowa ga ci gaban tattalin arzikin kasar.

An ce, ana fuskantar matsalar karancin wutar lantarki a yankunan karkarar kasar ta Zambiya, yawan wutar lantarkin da aka samar ga yankunan bai wuce kashi 4.4 cikin 100 ba. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China