Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin ya yi kira da a ciyar da shirin mika mulki gaba a Mali
2020-10-09 09:44:11        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa al'ummar kasar Mali wajen ciyar da shirin mika mulkin kasar gaba.

Zhang Jun ya ce, halin da ake ciki a kasar ta Mali bayan da wasu sojoji suka yi bore a ranar 18 ga watan Agusta, ya janyo hankalin kasashen duniya. Sai dai kuma a cewarsa, kasar Sin tana farin cikin sanar da cewa, an rantsar da shugaban rikon kwarya da mataimakinsa, an kuma nada firaminista, a hannu guda kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta yanke shawarar dage takunkumin da ta kakabawa kasar ta Mali.

Wakilin kasar ta Sin ya kuma shaidawa kwamitin sulhun MDDr cewa, kasar Sin tana maraba da wadannan nasarorin da aka cimma, ta kuma yaba kokarin da masu ruwa da tsaki a kasar da ma ECOWAS suka yi, na warware rikicin kasar cikin lumana. Sai dai har yanzu akwai manyan kalubale a gaba.

A don haka, ya ce, kasar Sin tana fatan dukkan bangarori a kasar ta Mali, za su dora muhimmanci kan muradun kasar da na jama'a a gaban komai, su hau teburin tattaunawa da yin hadin kai, su kuma dora kan ci gaban da aka samu, ta yadda za a ciyar da shirin mika mulkin kasar gaba yadda ya kamata.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China