Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin tsaron MDD ya sabunta takunkumin da aka kakabawa Mali
2020-09-01 09:48:52        cri

Yayin taron sa na jiya Litinin ta kafar bidiyo, kwamitin tsaron MDD ya amince da tsawaita wa'adin takunkumin da aka kakabawa kasar Mali da karin shekara guda. Daukacin mambobin kwamitin sun kuma amince da tsawaita wa'adin aikin kwamitin kwararru da aka kafa, domin sanya ido kan wannan batu.

Yayin da kwamitin ke amince kudurin mai lamba 2541 na shekarar 2020, ya kuma ayyana ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2021, a matsayin ranar karshe ta sabon wa'adin takunkumin.

Hakan ya kuma yi daidai da tanadin dake kunshe cikin shaidara ta 1 zuwa 7, ta kuduri mai lamba 2374 na shekarar 2017, wanda ya kunshi kakaba takunkumin daskaras da kadarorin masu kawo tsaiko, ga aiwatar da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da sasanto a kasar ta Mali.

Kaza lika bisa tanadin kudurin, an jaddada cewa, takunkumin da aka tanada zai shafi daidaikun mutane, da rukuni, ko kamfanonin da kudurin ya lasafta, bisa tanajin kuduri na 2374 na shekarar 2017. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China