Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhun MDD ya bayyana damuwa game da rikicin siyasar Mali
2020-07-28 11:32:35        cri

Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana matukar damuwa kan takkadamar siyasar kasar Mali, yana mai kira da a kai zuciya nesa.

Cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taro ta kafar bidiyo da kwamitin ya yi jiya, kan halin da kasar Mali ke ciki, mambobinsa sun bayyana cikakken goyon bayansu ga yunkurin da kungiyar ECOWAS ke yi na sulhunta bangarorin kasar, da kuma shawarwarin da shugabannin kasashen kungiyar suka gabatar yayin taron kolin da suka yi game da batun a jiya Litinin.

Mali ta tsunduna cikin takaddamar siyasa ne tun ranar 5 ga watan Yuni, lokacin da zanga-zanga ta barke a birnin Bamako. Gammayar 'yan adawa da kungiyoyin al'umma, na neman shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ya sauka daga karagar mulki.

Lamarin ya kara ta'azzara ne bayan an kashe masu zanga-zanga akalla 11, yayin da wasu 150 suka jikkata tsakanin ranar 10 zuwa 12 ga wata, a birnin Bamako. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China