Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya bukaci a kai zuciya nesa a Mali
2020-06-21 17:54:20        cri

Babban jami'in MDD Antonio Guterres, ya yi kiran a kai zuciya nesa bayan da aka samu barkewar rikicin siyasa a kasar Mali, a daidai lokacin da kasar ke fama da zanga-zanga da tarin matsalolin hare haren ta'addanci gami da tashe tashen hankula.

A sanarwar da ofishin yada labarai na sakatare janar din ya fitar, jami'in ya bayyana damuwa game da rikicin siyasa na baya bayan nan da ya barke a kasar Mali.

Sanarwar ta ce, Guterres ya bayyana cikakken goyon bayansa game da kokarin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ke gudanarwar a halin yanzu, musamman bisa ga kiran da kungiyar ta yi a ranar Juma'a, inda ta bukaci a gudanar da tattaunawa tsakanin dukkan bangarorin kasar Mali da nufin warware rikicin siyasar kasar.

Babban sakataren ya yi kira ga dukkan shugabannin siyasar kasar Mali da su gaggauta aika sakonnin neman zaman lafiya ga magoya bayansu, kana su kauce daukar duk wasu matakan da za su kara ruruta wutar rikicin kasar. Sannan ya jaddada muhimmancin tattaunawa ya kuma bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a kasar Mali da su zage damtse wajen yin aiki tare don tabbatar da doka da oda da mutunta hakkin dan adam.

Masu zanga zanga sun yi gangami a babban birnin kasar Mali, Bamako, a ranar 5 ga watan Yuni, inda suka yi gangami a manyan titunan birnin a ranar Juma'a domin neman shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ya yi murabus bisa zargin aikata rashawa.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China