Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya: GDPn yankin Saharan Afirka zai ragu zuwa kaso 3.3 a wannan shekara
2020-10-09 09:35:13        cri

Babban bankin duniya ya fitar da wani sabon rahoto jiya Alhamis dake nuna cewa, bunkasar tattalin arzikin kasashen Afirka dake yankin hamadar Sahara, za ta ragu da kaso 3.3 bisa dari a wannan shekara, idan an kwatanta da karuwar kaso 2.4 cikin 100 a shekarar 2019, sakamakon annobar COVID-19.

Rahoton ya ce, annobar COVID-19 ta yi babban tasiri kan harkokin tattalin arzikin kasashen Afirka dake wannan yanki, lamarin da ya cusa ci gaban tattalin arzikin kasashen yankin cikin hadari na tsawon shakaru 10.

Binciken da aka gudanar a nahiyar ta Afirka ya nuna cewa, annobar COVID-19 za ta jefa kimanin mutane miliyan 40 cikin kangin talauci, baya ga mayar da nasarorin a kalla shekaru biyar da aka cimma a fannin yaki da talauci baya.

A cewar rohoton na bankin duniya, matakan da aka dauka na dakile annobar, sun shafi tattalin arziki, kamar yadda ake iya ganin hakan a sassan duniya.

A cewar Albert Zuefack, babban masanin tattalin arziki na bankin duniya mai kula da shiyyar Afirka, hanyar farfadowa na iya zama mai dogon zango da kuma sarkakiya, amma aiwatar da managartan manufofi, da zuba jari da za su magance kalubale, da kara samar da karin guraben ayyukan yi da suka dace, za su gaggauta, da karfafa farfadowar kasashen na Afirka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China