Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu cutar COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 1.46
2020-09-29 10:42:45        cri

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai 1,460,084 ya zuwa ranar Litinin.

Hukumar yaki da cututtuka ta nahiyar ta fada cikin wata sanarwa cewa, adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a Afrika ya kai 35,445 ya zuwa tsakar ranar Litinin.

Sai dai a cewar Africa CDC, yawan mutanen da suka warke daga cutar a duk fadin nahiyar ya kai 1,206, 237.

Game da girman tasirin illar da annobar COVID-19 ke ci gaba da haifawa a kasashen Afrika kuwa, Africa CDC ta ce, kasashen da cutar ta fi shafa sun hada da Afrika ta kudu, Masar, Morocco, Habasha da Najeriya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China