Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tawagar aikin jinya da kasar Sin ta turo zuwa kasar Lesotho ta gama aikinta yadda ya kamata
2020-10-07 17:00:54        cri

 

A ranar 7 ga watan Oktoba, tawagar kwararrun likitoci masu yaki da cutar annobar COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta turo zuwa kasar Lesotho, ta cimma nasarar kammala aikinta, kuma ta tashi zuwa kasar Angola.

Yayin da tawagar kwararrun take aiki a kasar Lesotho, ta ziyarci asibitocin da aka kebe da nufin karbar masu fama da cutar COVID-19, kana da ba da horo ga ma'aikata masu aikin rigakafi da shawo kan cutar, da likitoci da nas nas, sun kuma yi musayar ra'ayi da more fasahohin da kasar Sin ta samu na yakar annobar tare da sassan kiwon lafiyar kasar, kuma sun ba da shawarwarin da suka dace da yanayin kasar ta Lesotho, wajen yakar cutar. Liu Zheng, shugaban kungiyar kwararrun ya bayyana cewa,

"Ta hanyar yin bincike a Lesotho don fahimtar halin da ake ciki, a karshe mun kaddamar da wani rahoto na kandagarki da shawo kan annobar. A cikin rahoton, mun kawo fasahohin kasar Sin, da na Hubei da kuma na Wuhan, hade da yanayin da ya dace da kasar Lesotho a fannonin kula da ayyukan sassan kananan hukumomi da gidauniyar kiwon lafiya. Muna fatan Lesotho za ta karfafa karfinta na binciken cutar, tare da jaddada kandagarki da sarrafa al'umma, mun kuma ba su shawarar koyo daga fasahohin da kasarmu ta samu. Baya ga haka, mun ba su shawarar cewa, ya kamata a kula da marasa lafiya da ke fama da annobar bisa bambancin halin da suke ciki. Misali, ana iya shigar da marasa lafiya da cutarsu ba ta tsananta ba zuwa asibitocin ba da kariya, kuma ana iya tattara marasa lafiya dake cikin mawuyacin hali a cikin asibitocin da aka kebe. Wadannan shawarwarin sun samu amincewa daga bangaren Lesotho."

A nasa bangaren, kasar Lesotho ta nuna godiya da yabo na gaske game da isar da tawagar kwararrun ta kasar Sin. Firaministan kasar ta Lesotho, Moeketsi Majoro da kansa ya yi maraba da isowar tawagar kwararrun kasar Sin filin jirgin sama.
Ya ce, kungiyar kwararrun kasar Sin za ta taimaka wa kasar ta Lesotho yadda ya kamata, wajen inganta matakan rigakafin cutar, tare da kara kwarin gwiwar jama'ar kasar wajen yaki da annobar. Cike da imani, ya bayyana cewa, tabbas kasarsa za ta iya cimma nasarar yakar cutar cikin gaggawa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China