Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana cikin wani lokaci mai muhimmanci na yakar cutar COVID-19 a nahiyar Afirka
2020-08-06 14:20:49        cri

Zuwa jiya Laraba, an samu mutane 980,832 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka. Cikin wadannan mutane 980,832 na kasashen Afirka daban daban, wadanda suka kamu da cutar COVID-19, akwai mutane 21,102 da suka mutu, yayin da aka samu warkewar wasu 656,040. Darekta mai kula da harkokin nahiyar Afirka a hukumar lafiya ta duniya WHO, Matshidiso Moeti, ta ce, ana cikin wani lokaci mai muhimmanci, a kokarin tinkarar cutar COVID-19 a kasashen Afirka, don haka ta bukaci kasashen nahiyar da su daidaita matakansu nan take, gami da baiwa kananan hukumomin cikakken ikon daukar matakan gaggawa domin hana bazuwar annobar.

A nasu bangare, kasashen Afirka suna kokarin kyautata fasahohinsu a fannin yakar annoba, inda galibinsu suka fara samar da marufin baki da hanci, da ruwan kashe kwayoyin cuta, da sauran kayayyakin da ake bukata, lamarin da ya nuna yadda kasashen Afirka suke dogaro da kansu wajen tinkarar cutar COVID-19.

A kasar Afirka ta Kudu, ministan kula da harkokin cinikayya da masana'antu na kasar, Ebrahim Patel, ya sanar a ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata cewa, an riga an kammala samar da na'urorin taimakawa numfashi a zargon farko, da kasar Afirka ta Kudu ta kirkiro gami da hada su, wadanda za a raba ma asibitocin kasar don biyan bukatun majiyyata. Hakan ya sa kasar ta zama ta farko a cikin kasashen Afirka, da suka fara samar da na'urorin taimakawa numfashi da kanta. Yanzu kasar Afirka ta Kudu tana da shirin samar da na'urorin taimakawa numfashi har dubu 20 kafin karshen watan nan na Agusta, wadanda za a raba su a cikin gida, gami da samar da su ga sauran kasashen dake nahiyar Afirka.

A kasar Kenya kuma, majalisar dattawan kasar, ta dakatar da tarukan kwamitocin ta daban daban har tsawon wata daya, don hana bazuwar cutar COVID-19. A nasa bangare, ministan lafiyar kasar, Mutahi Kagwe, ya ce an bude wata sabuwar cibiyar kula da masu kamuwa da cuta mai yaduwa, ko kuma wadanda lafiyar jikinsu ke cikin wani yanayi mai tsanani, a wani asibitin dake karkashin jami'ar Kenyatta. A cewarsa, wannan cibiya mai gadaje 500, za ta saukaka matsin lambar da asibitocin kasar ke fuskanta.

A kasar Uganda, an sanar da mutuwar mutane sakamakon cutar COVID-19 cikin kwanaki 3 a jere. Ban da haka, kwararrun lafiya na kasar sun ce, cutar na samun karin bazuwa tsakanin ungwannin kasar daban daban. Saboda haka, ministar watsa labarai da fasahohin sadarwa ta kasar, Judith Nabakuba, ta yi kira da a takaita gudanar da gangamin jama'a a lokacin da ake kamfe gabanin babban zabe.

Ban da haka, fasahohin kasar Sin su ma sun taka rawar gani, a kokarin kasashen Afirka na tinkarar annobar. A ranar 16 ga watan Yulin da ya gabata, gwamnatin kasar Angola da kamfanin BGI na kasar Sin, sun kulla wata kwangila, inda kamfanin zai gina wasu dakunan gwajin kwayoyin cutar COVID-19 guda 5 a kasar Angola, ta yadda za a baiwa kasar damar gudanar da gwaji kan mutane dubu 6 a kowace rana, jimillar da za ta karu daga wasu 600 da ake da su yanzu.

Ban da kasar Angola, kamfanin BGI na kasar Sin na kokarin taimakawa sauran kasashen da suka hada da Gabon, da Togo, da Botswana, wajen gina dakunan gwajin kwayoyin cutar COVID-19. Inda shugaban kasar Gabon Ali Bango Ondinba, ya taba ziyartar wani dakin gwajin da ake kokarin gina shi, tare da bayyana fatansa na ganin dakin ya taimaka ga kokarin tinkarar annoba a kasar.

Sa'an nan a kasar Zimbabwe, wasu jami'o'i da kamfanoni na kasar, suna kokarin samar da kayayyakin da suka hada da safar hannu, da marufin baki da hanci, da na'urorin binciken zafin jiki, da dai sauransu. Yayin da sojoji da 'yan sandan kasar su ma suka shiga aikin samar da kayayyakin da ake tsananin bukatarsu.

Ban da haka kuma, wani jami'in kasar ya taba bayyana fatansa, na samun hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin hada magungunan gargajiya, bisa la'akarin da yadda magungunan gargajiya ke taka rawar gani, a kokarin da kasar Sin take na dakile cutar COVID-19. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China