Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka na fuskantar babban kalubale a yayin da yawan masu harbuwa da COVID-19 ya zarce miliyan guda
2020-08-10 14:24:24        cri





A ranar 7 ga wata, yawan mutanen da suka harbu da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka, ya zarce miliyan daya. Ci gaban yaduwar annobar ya haifar da munanan illoli ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma na kasashen Afirka.

Alkaluman da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Afirka(Africa CDC) ta fitar sun yi nuni da cewa, ya zuwa jiya Lahadi, yawan mutanen da suka harbu da cutar COVID-19 a nahiyar, ya zarce miliyan 1 da dubu 30, a yayin da cutar ta yi ajalin mutanen suka kai dubu 22 da 966. A halin yanzu, cutar na ci gaba da yaduwa a akasarin kasashen Afirka.

Ofishin hukumar lafiya ta duniya da ke nahiyar Afirka ya bayar da labari a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata cewa, a watan Yulin, gaba daya yawan mutanen da suka harbu da cutar ya ninka har sau daya, hukumar ta kuma gargadi kasashen Afirka da kada su sassauta matakan kandagarkin cutar da suke dauka.

Kasar Afirka ta Kudu a halin yanzu ta kasance kasar da ta fi yawan mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar a nahiyar. A kwanan baya, Mr. Michael Ryan, jami'in da ke kula da al'amuran gaggawa na hukumar lafiya ta duniya ya bayyana cewa, saurin karuwar masu harbuwa da cutar a kasar ta Afirka ta Kudu wata alama ce ta barkewar cutar a fadin Afirka, ya kuma bayyana damuwarsa dangane da saurin yaduwar cutar a nahiyar ta Afirka.

A sa'i daya kuma, rahoton da bankin raya Afirka ya fitar a watan Yulin ya nuna cewa, tattalin arzikin Afirka ka iya faduwa da kaso 1.7% daga 3.4% a wannan shekara, a yayin da 'yan Afirka kimanin miliyan 24.6 zuwa miliyan 30 ka iya rasa guraben ayyukan yi. Lamarin da zai iya jefa 'yan kasashen Afirka kimanin miliyan 28.2 zuwa 49.2 cikin tsananin talauci a wannan shekara zuwa shekara mai zuwa.

A sakamakon matsi da ake fuskanta ta fannin dakushewar tattalin arziki, wasu kasashen Afirka sun fara farfado da sana'o'insu. Alkaluman da kungiyar tarayyar Afirka ta fitar a ranar 28 ga watan Yulin da ya gabata sun nuna cewa, ya zuwa lokacin, akwai wasu kasashen Afirka 31 da suka sassauta matakan da suka dauka na kandagarkin cutar, wadanda suka amince da wasu masana'antunsu da su koma bakin aiki sannu a hankali. A sa'i daya kuma, kasashen Kenya da Zambia da Namibia da Senengal da ma sauran wasu kasashen Afirka sun gabatar da matakai da shirye-shirye iri iri na sa kaimin bunkasuwar tattalin arziki.

Duk da haka, farfadowar harkokin tattalin arziki ta kuma haifar da barazana ga ayyukan kandagarkin annobar. Masharhanta sun yi nuni da cewa, yadda za a kai ga kiyaye daidaito a tsakanin aikin farfado da tattalin arziki da kuma kandagarkin cutar su ne kalubale da ke gaban kasashen Afirka da dama.

A halin yanzu, kungiyoyin duniya na samar da gudummawa ga kasashen Afirka da ke kokarin yaki da annobar. A ranar 27 ga watan Yulin da ya gabata, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya amince da samar da rancen kudin da ya kai dala biliyan 4.3 ga kasar Afirka ta Kudu, don a samar da guraben aikin yi a kasar da kuma tallafa wa masana'antun da annobar ta shafa. A wannan rana kuma, hukumar lafiya ta duniya ta sanar da samar da na'urorin gwajin cutar COVID-19 2000 da kuma na'urar daukar samfura 7000 ga kasar Mozambique.

A sa'i daya kuma, tun bayan bullar cutar a nahiyar Afirka, kasar Sin da ma sauran kasashen duniya sun yi ta kokarin samar mata da gudummawa. Bayan da aka gano bullar cutar a karo na farko a nahiyar Afirka a ranar 14 ga watan Faburairun bana, gwamnatin kasar Sin da ma kungiyoyin jama'a na kasar sun yi ta samar wa kasashen Afirka kayayyakin kadagarkin cutar gami da sauran tallafi. A yayin taron kolin hadin kan Sin da Afirka na yaki da annobar da aka gudanar a watan Yunin da ya gabata, kasar Sin ta kuma yi alkawarin samar wa kasashen Afirka alluran rigakafin cutar da zaran ta kammala nazarin alluran da kuma fara amfani da su.

Darektan cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Afirka John Nkengasong a kwanan baya ya bayyana cewa, in dai kasashen Afirka za su iya daukar matakai makamantan na Sin da sauran kasashe suka dauka, hakika za su iya kai ga shawo kan cutar, don haka, akwai bukatar kulla huldar abokantaka ta kut-da-kut a tsakanin kasashen.

Darektan ya kara da cewa, duk da saurin karuwar yawan masu kamuwa da cutar a Afirka, za a ga cewa, har yanzu akwai kasashe sama da 30 da yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar bai kai 5000 ba, a yayin da a wasu kasashe sama da 40, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar bai kai dubu 10 ba. Don haka, idan har kasashen duniya suka yi hadin gwiwa kamar yadda ya kamata, babu tantama za a shawo kan annobar a nahiyar Afirka.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China