Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala taron UNGA 75 tare da cimma matsaya kan goyon bayan hadin gwiwar bangarori daban daban
2020-09-30 11:44:30        cri

An kammala taron babbar muhawara na babban taron MDD karo na 75 wato UNGA 75, a ranar Talata, a helkwatar MDD dake birnin New York, inda yawancin shugabannin kasashen duniya da wakilan kasa da kasa suka bayyana goyon bayansu kan hadin gwiwar bangarori daban daban karkashin tsarin MDDr.

Shugaban taron na UNGA Bozkir ya bayyana kyakkyawan fata cewa, nan da shekara ko watanni masu zuwa, yana da kwarin gwiwa mambobin kasashe da shugabanninsu za su goya masa baya wajen cimma wannan buri.

Da yake magana game da batutuwa uku wadanda yake son cimmawa a wa'adin jagorancinsa, Bozkir ya ce, na farko, amfani da gargadi a matakin farko, wato samar da matakan kandagarkin yaduwar cututtuka, na biyu, yin hadin gwiwa wajen tinkarar matsaloli, na uku, tabbatar da daidaito wajen samar da allurar rigakafin COVID-19 a nan gaba.

A lokacin dandali na musamman na babban taron MDD game da batun annobar a wannan shekara, shugaban taron ya bukaci masu ruwa da tsaki su gabatar da dabarun warware wadannan batutuwa uku, su karfafa hadin gwiwa, kuma su tafiyar da al'amurran duniya bisa hanya mafi dacewa domin cimma nasarar muradun samar da dawwammman ci gaba na MDD wato SDGs. Ya yi kira da babbar murya na neman rarraba allurar rigakafin annobar bisa tsarin daidaito a duniya.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China