Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban AU ya bukaci a gudanar da huldar bangarori daban daban a tsarin shugabancin duniya
2020-09-25 09:33:49        cri

Shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU, Moussa Faki, ya bukaci a farfado da huldar bangarori daban daban a kokarin da duniya ke yi na tabbatar da ingantaccen tsarin shugabanci a duniya.

Ya ce, bullar wannan annobar ta COVID-19 ta kara bayyanawa a fili cewa, dukkan 'yan adam iyali guda ne wadanda ba za a taba raba su ba. Annobar ta nuna cewa, ra'ayin bangare guda ba shi da wani alfanu, ya bayyana hakan ne a babban taron mahawara na kwamitin sulhun MDD game da sha'anin tafiyar da shugabancin duniya bayan annobar COVID-19.

Faki ya ce, annobar ta kara share hanyar tabbatar da tsarin gamayyar bangarori daban daban, da kuma bayyana rashin alfanun kafa shinge da wasu mambobin kasashe ke kokarin yiwa 'yan adam wadanda tamkar iyali guda ne.

Ya ce, Afrika ta bukaci kowane bangare ya nuna jajurcewa kuma a yi aiki tare da juna wajen tabbatar da farfadowar tsarin gamayyar bangarori daban daban, wanda shi ne manufar kungiyar AU.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China