2020-09-25 10:48:18 cri |
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bukaci kwamitin sulhun MDDr ya samar da wata kakkarfar dangantaka da hanyoyin tattaunawa a kai a kai tsakaninsa da kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika AU, domin daga matsayin aikin wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afrika.
Guterres, ya fadawa babban taron mahawara na kwamitin sulhun MDDr game da batun shugabancin duniya bayan annobar COVID-19 cewa, wannan mataki zai bayar da kyakkyawar damar sauke nauyi, inda kungiyar AU za ta samu damar aiwatar da ayyukan wanzar da zaman lafiya, da yaki da ta'addanci, wanda kwamitin sulhun MDDr ke goyon bayan ayyukan, tare da tabbacin samun kudaden gudunmawar da ake tattarawa don gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya.
Ya ce, wannan ce kadai hanyar da za a gina tsarin gamayyar da ake bukata wajen kawar da ayyukan ta'addanci a nahiyar Afrika, da kuma cimma burin aiwatar da shirin wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU na kawar da amon bindiga daga nahiyar.
Jami'in MDDr ya ce, akwai bukatar dunkulewa don tabbatar da hadin gwiwar bangarori daban daban wanda zai dace da kakkarfar dangantaka da hadin gwiwa a tsakanin hukumomin kasa da kasa da na shiyya shiyya, da hukumomin kudi na kasa da kasa, da sauran bangarorin kawance da cibiyoyi na duniya.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China