Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yabawa ci gaban da bangarorin Libya suka samu a tattaunawar Masar
2020-09-29 10:12:30        cri

Ofishin shirin MDD dake kasar Libya UNSMIL, ya yabawa irin nasarorin da aka cimma da irin halayyar da wakilan bangarorin kasar Libya suka nuna a lokacin gudanar da tattaunawar tsaro da al'amuran sojoji da aka gudanar a Masar.

Sanarwar da UNSMIL ya fitar ta ce, tawagar sojoji da 'yan sanda daga gabashi da yammacin Libya sun fara taron tattaunawar tsaro da al'amurran soji, karkashin yarjejeniyar tattaunawar hadin gwiwar sojoji ta 5+5 Joint Military Commission.

UNSMIL ya mika sakon godiya ga gwamnatin Masar sakamakon shirya muhimmiyar tattaunawar. Kana ya yabawa wakilan bangarorin biyu bisa yadda suka nuna halayyar sanin ya kamata a tattaunawar wacce aka shirya da nufin kawo karshen tashe tashen hankula a tsakiyar Libya.

Ofishin MDDr dake Libya yana fatan sakamakon da za a samu a tattaunawar ta gaba da gaba, zai kasance a matsayin share fagen shiga hakikanin tattaunawar hadin gwiwar 5+5.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China