Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi watsi da yunkurin dakatar da manhajar Tik Tok a Amurka
2020-09-29 15:51:00        cri
A ranar 27 ga watan Satumba, agogon kasar, wata kotun tarayyar Amurka dake gundumar Columbia, ta yanke hukuncin watsi da yunkurin gwamnatin Amurka na aiwatar da dokar ofishin shugaban kasa na neman dena amfani da manhajar Tik Tok a wayoyin a hannu a Amurka.

A cewar rahoton da radiyon al'umma na kasar Amurka ya watsa, a lokacin sauraron shara'ar a ranar 27 ga wata, babban lauyan dake kare manhajar Tik Tok John Hall, ya bayyana cewa, Tik Tok yana da abokan mu'amala kusan miliyan 100 a Amurka, kuma wani bangare ne na tsarin yanar gizo. Don haka rufe manhajar Tik Tok babu wani abu da zai sauya. Kuma matakin ya saba 'yancin mutanen kasar na ikon da suke da shi na yin magana.

Game da batun bukatar da sashen shari'a na Amurka ya bukata cewa, dakatar da manhajar Tik Tok yana da alaka ne da batun tsaron kasa, Hall ya ba da rahoton cewa, a halin yanzu babu wata kwakkwarar hujja dake tabbatar da cewa manhajar Tik Tok barazana ce ga tsaron kasar Amurka, sai dai ma batun na Tik Tok ya kara tada kura a fagen siyasar kasar Amurka. Haramta amfani da manhajar dai dai yake da rashin iya bibiyar tsarin sadarwa, lamarin bai ci karo da batun tsaron kasa ba, sai dai baya daga cikin dalilan da za a iya kafa hujja dasu kan batun babban zaben kasar dake tafe. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China