2020-08-06 14:30:56 cri |
Kwanan baya, firaministan Austriliya Scott Morrison ya halarci dandalin tsaro na Aspen na Amurka, inda ya nuna cewa, babu wasu shaidu dake bayyana cewa, ya kamata a hana amfani da manhajar Tik Tok a Austriliya.
A nasu bangare, wasu kasashe 3 mafi karfin tatattalin arziki na Turai ba za su daina amfani da Tik Tok ba, duk da cewa, kasar Amurka take kara matsa lamba kan kamfanonin kimiya da fasaha na kasar Sin.
Ban da wannan kuma, kafar yada labarai ta Bloomberg ta ba da labari cewa, gwamnatin Birtaniya ta yarda kamfanin Byte Dance wanda ke mallakar Tik Tok ya bude reshensa a London.
Matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kuntatawa Tik Tok ya gamu da zargi matuka daga masana doka da shari'a na jami'ar Yale, Stanford da dai sauransu. (Amina Xu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China