Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai bukatar amincewar Sin game da wani sashi na batun sayar da Tik Tok
2020-08-31 10:56:53        cri

Kwararren malami a fannin hada hadar cinikayya da tattalin arziki Cui Fan, ya ce akwai bukatar amincewar bangaren Sin, game da batun cinikayyar fasahar dandalin yada gajerun faya-fayan bidiyon na Tik Tok mallakin kamfanin ByteDance, kamar yadda hakan ke kunshe cikin wasu ka'idoji da aka yiwa gyara masu nasaba da hakan.

Cui Fan wanda ke koyarwa a jami'ar kasuwanci da tattalin arziki ta kasar Sin, ya ce sabon tanadin ka'idojin cinikayyar fasahohin sadarwar ya shafi kamfanonin da aka yiwa kaidi, ko aka sanyawa takunkumin mika fasahohin su ga ketare. Kalaman masanin na zuwa ne, yayin da ake tattauna batun shirin sayar da Tik Tok ga kamfanin kasar Amurka.

A matsayin ByteDance, na kamfani mai kirkirar sabbin fasahohin sadarwa na zamani, da kwarewa a fannin kwaikwayon tunanin bil Adama da ma sauran fannoni, wasu daga fasahohin sa sun fada rukunin wadannan sabbin ka'idoji.

Ma'aikatun cinikayya, da na kimiyya da fasaha na Sin, sun kara sassa 23, cikin fannonin fasahohin da ke da kaidi, ko aka haramta mallaka su ga kamfanonin waje, aka kuma sanar da hakan a Juma'ar makon jiya.

A cewar Cui Fan, muhimman sassa biyu da cinikayar Tik Tok suka shafa, su ne bangaren fasahar tattara bayanai ta hanyar nazartar alkaluman da aka tattaro, da kuma fannin cudanyar bayanai masu nasaba da fasahar kwaikwayon tunanin bil Adama. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China