Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Somalia da WFP sun kulla yarjejeniyar dakile tasirin farin-dango
2020-09-28 10:35:48        cri

A jiya Lahadi ne gwamnatin kasar Somalia, ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da shirin abinci na duniya WFP, wadda za ta kunshi tsarin dakile mummunan tasirin da farin-dango suka yiwa sashen noma, da samar da abinci na kasar.

Ministan kwadago da walwalar jama'a na kasar Sadik Warfa, ya ce yarjejeniyar ta tanaji aiwatar da matakan gaggawa na rage radadin da al'umma, musamman matalauta ke fama da shi sakamakon bullar farin-dango a kasar, ta hanyar samar musu da abubuwan bukata, ciki har da kayan abinci a gajeren zango, tare da daukar matakan kare rayukan su, da inganta samun kudaden shiga ta hanyar bayar da kudaden tallafi na kai tsaye.

Jami'in ya kara da cewa, gwamnatin kasar ta yi namijin kokari, wajen kaiwa ga iyalai da matsalar farin-dango ta shafa, kuma ana sa ran sabon shirin zai amfani iyalai da dama a gundumomi 43 mafiya fama da wannan matsala.

Wannan mataki na zuwa ne, bayan da gwamnatin Somaliyar ta amshi kudade da yawan su ya kai dala miliyan 40 daga bankin duniya, don taimakawa mazauna yankunan karkara daga gundumomi 43 dake sassan kasar daban daban, karkashin shirin na watanni 6. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China