Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Somaliya ya nada sabon firaminista
2020-09-18 19:50:58        cri

Shugaban kasar Somaliya Mohamed Farmajo, ya nada Mohamed Hussein Roble, a matsayin sabon firaministan kasar, inda ya maye gurbin Ali Hassan Khaire wanda majalisar dokokin kasar ta tsige a watan Yulin wannan shekara.

Farmajo, ya sanar da nadin sabon firaministan ne jiya da dare, inda ya umarni Roble da ya kafa sabuwar gwamnati, da za ta jagoranci kasar wajen mika mulki, yayin da Somaliyar ke shirin gudanar da babban zaben kasar na shekarar 2020/2021.

Shugaban ya ce, ya nada Roble ne, saboda yana da ilimi da kwarewa, zai kuma iya aiwatar da shirin gwamnati, na kokarin ginawa da tsara shirye-shiryen raya kasa. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China