Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kimanin mutane 37,000 ambaliyar ruwa ta shafa a Somaliya
2020-07-22 11:34:40        cri

Ma'aikatar kula da jin dadin al'umma a Somaliya, ta ce ruwan sama mai karfin gaske da ya haddasa ambaliyar ruwa, ya haifar da kalubalen rayuwa da yanakin jin kai ga kimanin mutane 37,000 a kasar.

Cikin sanarwa da ma'aikatar ta fitar a jiya Talata a birnin Mogadishu, ta ce ambaliyar ruwan ta dakatar da hada hadar kasuwanci, ta katse layukan sadarwa, da tituna, ta kuma gurgunta yanayin walwalar al'ummu da dama.

Kasar Somaliya dai na fama da kalubalen cutar numfashi ta COVID-19, da farin dango masu cinye amfanin gona a wasu yankunanta dake arewaci, baya ga ambaliyar ruwa da a yanzu ke kara dagula al'amura. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China