Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kai hari wani sansanin sojan Somalia
2020-08-08 17:17:35        cri

An kai hari wani sansanin soji dake birnin Mogadishu na Somalia da sanyin safiyar yau Asabar.

Wani ganau ya ce an ji karar fashewar abu a kusa da mahadar Bar-Ayaan dake lardin Wardhigley na Mogadishi, bayan wani dan kunar bakin wake ya tuka wata motar dake shake da ababen fashewa zuwa cikin wani sansanin soji.

A baya-bayan nan, dakarun gwamnatin kasar sun matse kaimi wajen kai hare-hare kan mayakan al Shabab a yankin kudancin kasar, inda mayakan ke boye a kauyuka suna kai harin kwantar bauna tare da dasa nakiyoyi. Wani harin soji a ranar Alhamis, ya kashe mayakan kungiyar 6 a yankin Lower Juba dake kudancin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China