Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alkalin kotun tarayyar Amurka ya dakatar da umarnin shugaba Trump game da haramta TikTok
2020-09-28 10:08:17        cri

Wani alkalin babbar kotun tarayyar Amurka, ya dakatar da umarnin da shugaba Dornald Trump ya gabatar, game da haramtawa kamfanin nan na yada kananan faya fayan bidiyo na TikTok na kasar Sin gudanar da ayyukan sa a Amurka.

Kotun dai ta dakatar da umarnin shugaban na Amurka ne a jiya Lahadi, 'yan sa'o'i gabanin cikar wa'adin fara aiki da umarnin.

Bayan sauraran karar da aka gabatar ta wayar tarho, mai shari'a Carl Nichols na kotun tarayyar dake gundumar Columbia, ya ba da umarnin dakatar da aiki da dokar shugaban kasar, umarnin da ya tanaji dakatar da masu amfani da manhajar daga sauke karin da aka yi mata. Tun da fari, kamfanin dake mallakar TikTok wato ByteDance, ya gabatar da bukata ga kotun, da ta baiwa kamfanin mai mazauni a birnin Los Angeles, damar ci gaba da ayyukan sa ba tare da wata tangarda ba, zuwa a kalla lokacin da kotun za ta yi cikakken zaman sauraron karar.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China